Gwamnatin jihar Kaduna ta sassauta dokar hana fita da aka saka a birnin Kaduna da Zaria.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida Samuel Aruwan ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar yau.
Ya ce wamnatin ta cire hana fita daga ƙarfe ƙarfe 08:00am na safe zuwa ƙarfe 06:00pm na yamma bayan sassauta wa da aka yi daga awanni 24.

Gwamnatin ta saka dokar hana fita tsawon awanni 24 a Zaria da birnin Kaduna bayan da aka samu hargitsi yayin zanga-zangar yunwa a jihar.

Lamarin da ya kai ga farwa kadarorin gwamnati da kayan jama’a.
Sai dai gwamnatin ta sassauta dokar a yau bayan da aka yi wani zama da masu ruwa da tsaki a harkokin tsaro a jihar.
Gwamnatin ta ce an samu ci gaba a al’amuran tsaro a jihar wanda hakan ya sanya aka cire dokar.
Sai dai jami’an tsaro za su ci gaba da sanya idanu dangane da al’amuran jama’a don ganin ba’a kawo cikas ga zaman lafiya a jihar ba
Haka kuma ba za su lamunci wani gangami ko taro a jihar ba wanda zai haifar da tarzoma ko rikici da zai taɓa zaman lafiya a jihar.