Wasu Rahotanni sun bayyana cewa an samu wata ambaliyar ruwa a wasu yankuna da dama na ƙaramar hukumar Madagali ta Jihar Adamawa, wanda hakan ya haifar da asarar rayuka da kuma dukiyoyi masu tarin yawa.

Rahotanni sun tabbatar da cewa ambaliyar ta yi sanadiyyar rasa rayukan mutane shida, ya yi da ta raba fiye da mutane 2,000 da muhallansu, tare kuma da lalacewar gonaki, da gadoji masu yawa.

Daga cikin guraren da ambaliyar ta shafa sun hada da Kichinga wanda ya kasnce garin gwamnan Jihar Ahmad Fintiri, sai Mildu, Maradi, Mayo Wandu, Shuware, Pambla 2 da Palam.

Shugaban karamar hukumar ta Madagali Hon Simon Musa ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce ambaliyar ta bana ta shafi guraren da ba a taba fuskantar matsalar ta ambaliyar ba.

Musa ya kara da cewa daruruwan mutane da ambaliyar ta raba da matsugunnansu a halin yanzu suna zaune ne a sansani Goma na wucin gadi da wanda aka kafa domin taimaka musu.

Shugaban ya ci gaba da cewa mbaliyar ta faru ne bisa mamakon ruwan sama mai ƙarfi da aka tafka a kan Dutsen Mandara, wanda hakan ya haifar da zaizayar ƙasa da lalata Gadar Shuwa, gidaje, kayan abinci, da kuma gonaki.

Musa ya kuma yi kira ga gwamnatin Tarayya da gwamnatin Jihar da kuma kungiyoyin agaji da su kaiwa yankunan daukin gaggawa domin fitar da su daga matsalar.

Hakimin Shuwa Mustafa Muhammad Sanusi ya bukaci da gwamnatin jihar da ta gaggauta kaiwa yankunan dauki.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: