Gwamnan Jihar Kogi Ahmad Usman Ododo na jam’iyyar APC ya yi kira ga ‘yan adawa a Jihar da su zo su hada kai domin ganin sun ciyar da Jihar gaba.

Gwamnan ya bayyana hakan ne Hakan ne ta cikin wata sanarwa da mai bai’wa gwamnan shawara na musamman kan harkokin yada labarai Ismail lsah ya fitar a yau Asabar.
Sannan gwamnan ya kuma yaba da hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke wanda ya tabbatar da nasararsa ta zama halastaccen gwamnan jihar.

Ododo ya bukaci magoya bayansa da kuma mambobin jam’iyyarsu ta APC da su gudanar da bukukuwan murnar samun nasararsa cikin natsuwa da kwanciyar hankali.

Gwamnan ya ce nasarar da ya samu nasara ce ta al’ummar jihar da suka fito suka kada masa kuri’a a ranar 11 ga watan Nuwamban 2023.
A jiya Juma’a ne dai kotun Kolin Najeriya ta tabbatar da Ododo a matsayin zababben gwamnan Jihar ta Kogi, inda ta yi watsi da karar da jam’iyyar SDP ta shigar gabatan tana mai kalubalantar nasarar Ododo,