Kungiyar Dattawan Arewa NEF ta yi Allah wadai da hallaka Sarkin Gobir Alhaji Isa Bawa a jihar Sokoto bayan ‘yan bindiga sun yi garkuwa da shi.

Daraktan yada labaran kungiyar Abdulaziz Suleiman ne ya bayyana hakan a jiya Juma’a ta cikin wata sanarwa da ya fitar.

Kungiyar ta nuna damuwa kan yadda ayyukan yan ta’adda ke kara karuwa aKasar.

Kungiyar ta bayyana cewa kisan na sarkin Gobir ya keta darajar sarakunan Kasar.

Acewar sanarwar hallaka sarkin na Gobir ba iya keta darajar sarakuna ya yi ba, hakan ya nuna cewa yankin Arewa na cikin halin tsaka mai wuya da ya ke neman daukin gaggawa.

Sanarwar ta ce kisa da aka yiwa Isa Bawa kisa ne na rashin imani da abin takaici wanda hakan ya zubar da martabar masarautun gargajiya da al’adun yankin na Arewa.

Kungiyar ta kuma bukaci masu ruwa da tsaki da sauran jami’an tsaro da su tabbatar da ganin an binciko wadanda suka aikata mummunar aika-aikar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: