Rundunar ’yan sandan ta kasa ta tabbatar da ceto daliban da ke karantar aikin lafiya 20 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a Jihar Benue.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ’yan sanda ta Kasa Olamuyiwa Adejobi ya fitar a yau Asabar.
Kakakin ya ce an kubtar da daliban ne ta ba tare da an biya kudin fansa ba, kamar yadda wasu rahotanni ke cewa sai da aka biya kuɗin fansa kafin sakin daliban.

Sanarwar ta bayyana cewa an kubatar da daliban aikin lafiyar ne su 20 a jiya Juma’a tare da karin wasu mutane da ke hannun masu garkuwar, a dajin Ntunkon da ke Jihar ta Benue.

Adejobi ya kara da cewa an ceto daliban ne ta hanyar amfani da kayan aiki na zamani da jirage masu saukar ungulu.
Sanarwar ta bayyana cewa rundunar na mika sakon godiyarta ga ofishin mai bai’wa shugaban kasa shawara na musamman kan sha’anin tsaro, da kuma al’ummar yankin da lamarin ya faru bisa kokarin da suka wajen ganin an kubtar da daliban.
An dai sace daliban Jami’ar Maiduguri da ta garin Jos ne a ranar Alhamis 15 ga watan Agustan nan a lokacin da suke kan hanyarsu ta halartar wani taron kungiyar Daliban Likitoci na shekara-shekara wanda za a gudanar a Jihar Enugu.