Ministan tsaro a Najeriya Muhammad Badaru Abubakar ya bayar da tallafin naira miliyan 20 ga mutanen da ambaliyar ruwa ya shafa a Jigawa

Badaru ya mika tallafin ga gwamnan jihar tare da jajantawa a dangane da ibtilain da ya faru yayin da ya je ziyarar jaje a jihar.


Hakan na kunshe a wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na ma’aikatar tsaro a Najeriya ya fitar.
Badaru ya bayyanawa gwamnan cewar gwamnatin tarayya na iya kokarinta don ganin ta tallafawa wadanda lamarin yashafa.
Amma wannan tallafi shi ya bayar daga aljihunsa don rage radadi.
Gwamnan jihar Umar Namadi ya yabawa ministan a bisa hanzarin tallafin da ya kai musu.
Sannan ya jinjina masa dangane da kokarin kulawa da al’ummar jihar