Jami’an ƴan sanda biyu ake zargi sun rasa ransu yayin da wasu su ka jikkata a sakamakon arangamar da su ka yi da mabiya mazahabar Shia a Abuja.

 

Ana zargin an harbe wani farar hula guda.

 

A yayin arangamar an kone motocin yan sanda uku.

 

Wani shaidar gani da ido ya tabbatar da cewa waɗanda su ka jikkata an yi gaggawar kai su asibiti da ke Zone 3 a Abuja.

 

Mabiya Shia dai na tattakin arba’in wanda su ka saba yi bayan ashura.

 

Ana zargin an fara jifan jami’an yan sandan da duwatsu tare da kwace bindigun yan sandan sannan su ka cinnawa motocinsu wuta.

 

Mai magana da yawun yan sanda a Abuja Josephine Adeh ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce an kashe ƴan sanda biyu sannan uku sun jikkata haka kuma an kone motocin yan sandan guda uku.

 

Kwamishinan ƴan sanda a Abuja ya sha alwashin dawo da komai yadda ya kamata yayin da su ke ci gaba da aikin tabbatar da tsaro.

Leave a Reply

%d bloggers like this: