Dubban mutane ne su ka ci cak da ababen hawansu tare da yin fiton matafiya a babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Lamarin ya fara ne a Katari kilomita 75 zuwa Abuja.

Da farko ana zargin manyan motoci guda biyu ne su ka fadi lamarin da ya saka tilas manyan motoci su ka yi jeren gwano a hanyoyin tafiya d dawowa.

Fasinjoji da dama ne su aka yi fitonsu don tafiya Abuja ko Kaduna.

A sakamakon cincirondon mutane, an jibge sojoji wadanda ke ƙoƙarin daidaita hanyar.

Lamarin ya faru ne a jiya Litinin wanda ya hifarwa matafiya da dama su k kwana a hanyar.

Matashiya TV ta hango jami’an soji da dama na ƙoƙarin ganin an samarwa matafiya hnya.

Katari dai na daga cikin hanyoyin da ba a karasa aikin titin ba kum yake barazana ga matafiya daga masu garkuwa da mutane.

Leave a Reply

%d bloggers like this: