Rundunar ‘yan sandan Jihar Neja ta tabbatar da hako wasu bama-bamai da aka binne a wasu gurare daban-daban na Jihar.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar Wasiu Abiodun ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Litinin.
Abiodun ya ce koda a tsakanin shekarar 2021 zuwa shekarar 2023 jami’annsu sun gano wasu ababan fashewa a yayin ayyukan yaki da ta’addanci a Jihar.

Jami’in ya ce daga cikin guraren da aka tono abubuwan fashewar sun hada da Galadiman-Kogo, da ke cikin karamar hukumar Shiroro, Mutun daya, a Mangu, da kuma Unguwar Gbeganu a garin Minna babban birnin Jihar.

Kakakin ya kara da cewa a karamar hukumar Shiroro a Jihar a yankin Galadima-Kogo tashin bam ya yi mummunar ɓarna a shekarar 2022, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar jami’an tsaro farin kaya na NSCDC.
Acewar Abiodun jami’an rundunar hadin gwiwa ta ‘yan sanda da kuma sauran jami’an tsaro ne suka gano wadannan bama-baman da aka binne su a gurare daban-daban na Jihar.
Kazalika kakakin ya bayyana cewa tuni ana lalata dukkan abubuwan fashewar da bama-baman da aka tono.
Wasiu Abiodun ya ce kuma ce an lalata kayayyakin ne a ranar 22 ga watan Agustan shekarar na a wani guri da ke bayan Zuma Rock a Suleja da ke Abuja.
Kakakin ya ce babban jami’im sashin kwance bama-bamai na rundunar ƴan sandan SP Muhammad Mamun ne ya jagoranci lalata bama-baman.