Rundunar ƴan sanda a jihar Yobe ta fara bincike kan zargin wani jami’in dan sanda da a cakawa wani wuka a kan naira 200.

Kwamishina yan sanda a jihar Garba Ahmed ne ya bayar da umarnin wanda ake zargin jami’in mai suna Mohammed Garba da k aiki a sansanin ƴan sandan kwantar da tarzoma na 41 da ke Damaturu a jihar.

A wata sanarwa da mai magana da yawun yan sanda a jihar ya fitar, ya ce lamarin ya aru ne a ranar 29 ga watan Satumba da ya gabata.

Hatsaniyar ta faru tsakanin jami’in da wani mai suna Abdulmalik Dauda.

Daka karshe dai an zargi ɗan sandan da caka masa wuka wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwarsa.

Rundunar ta ce ba za ta lamunci irin wannan rashin daar ba kuma za su tabbatar an yi adalci a kai.

Leave a Reply

%d bloggers like this: