Kamfanin rarraba hasken Wutar Lantarki na Kasa TCN ya bayyana cewa babu tsayayyen lokacin dawo da hasken wutar lantarki a yankin Arewa bayan lalacewar wutar.

Kamfanin ya cewa duk da cewa yana iya bakin kokarinsa wajen ganin ya gyara wutar, amma matsalar rashin tsaron da ake fama da ita a Kasar, hakan ba zai bayar da damar ci gaba da gudanar da gyaran da aka fara ba.

Babbar jami’ar Kamfanin Nafisa Asabe Alice ta bayyana hakan, inda ta tabbatar da cewa, kamfanin ya dakatar da gyaran ne bayar samun wata wasikar gargadi da yayi daga ofishin mai bai’wa shugaban Kasa Shawara na musamman kan tsaro, inda takardar ta bayyana cewa akwai babban hadari na rashin tsaro a yankin da aka samu lalacewar layin wutar uku.

Nafisa ta ce duk da cewa kamfanin na TCN ya riga da ya gama hada kayan aikin gyaran layin wutar, amma matsalar rashin tsaro ba za ta bashi damar shiga yankin da aka samu matsalar ba, har sai yaji ta bakin hukumomin tsaro.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: