Wasu rahotannin na nuni da cewa, bayan ci gaba da fuskantar rikice-riciken cikin gida da ake ci gaba da fuskanta a jam’iyyar NNPP a Kano, gwamnan Jihar, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya daina daga Wayar uban gidansa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.

Rahotanni sun bayyana cewa daga cikin abubuwa da suka kara rura wutar rikicin jam’iyyar ciki harda batun nada Kwamishinoni.
Hakan ya sanya gwamna Abba Kabir ya gujewa haduwa da jagoran nasa Rabi u Kwankwaso.

Sai dai bayan bullar takun sakar da ya fara shiga tsakanin Kwankwaso da Abba, gwamnatin Jihar ta Kano ta fito ta musantan jita-jitar da ke yawo cewa baraka ta kunno kai tsakanin gwamnan Jihar Injiniya Abba Kabir Yusuf da ubangidansa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, har ta kai ga baya daga wayarsa.

Hadimin gwamnan na musamman kan shafukan sada zumunta Salisu Yahya Hotoro ne ya bayyana hakan ta cikin wata wallafa da yayi a shafinsa na facebook a yau Litinin.
Hadimin gwamnan ya bayyana cewa ko kadan babu kanshin gaskiya a cikin rahotannin da ake yadawa akan Kwakwaso da Abba.
Acewar Hotoro har yanzu akwai alaka mai karfi tsakanin Kwankwaso da Abba, babu wani abu da ta shiga tsakaninsu.
Gwamnatin ta Kano ta bukaci mutane da su yi watsi da jita-jitar da ba ta da tushe balle makama.