Ministan Sadarwa na Najeriya Bosun Tijjani yayi wata ganawa da Kamfanonin sadarwa ta Kasar a birnin tarayya Abuja a yau Laraba.

Ministan yayi ganawar ne da kamfanonin MTN, Airtel, Glo, da kuma 9mobile da dai sauransu.
Ganawar ta mayar da hankalin ne akan yadda kamfanonin ke kokarin yin karin a kudin kira tura sako da kuma data a fadin Kasar, sakamakon tsadar al’amuran da ake fama dashi a Kasar.

Taron ya samu halartar masu ruwa da tsaki a fannin sadarwa da kuma hukumomin gwamnati, ciki har da hukumar kula da harkonin sadarwa ta ta Kasa NCC da hukumar bunkasa fasahar sadarwa ta kasa NITDA.

Kamfanonin dai na neman gwamnatin tarayya ta sahale musu yin karin kudin ne sakamakon halin matsin da ake fuskanta.