Gwamnan Jihar Sokoto Ahmad Aliyu ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta fadada shirin ciyarwa da ta ke yi a watan Azumin Ramadan da ke Tafe, don ciyar da mabukata a Jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a jiya Juma’a, a yayin kaddamar da wani Masallacin Juma’a a Ruggar Wauru wanda aka kammala gyaransa.
Acewar gwamnan tuni gwamnatinsa ta yi nisa wajen gudanar da shirye-shiryen Azumin Ramadan na Bana, inda ta ce gwamnatinsa za ta kara yawan abincin da ake dafa, don ciyar da mabukata a fadin Jihar.

Gwamna Aliyu ya kara da cewa a bana shirin ciyarwar zai tsallaka zuwa wasu yankuna na Jihar, inda za a bude guraren ciyawar da babu a yankunan nan.

Gwamnan ya kuma ci a wannan karo za a kara inganta shirin sosai don samar da abinci mai kyau, fiye da yadda ake yi a baya.
A karshe gwamnan ya ce gwamnatinsa ta himmatu wajen ginawa tare da gyara masallatai da kuma makarantun Islamiyya a fadin Jihar ta Sokoto.