Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Guo Jiakun ya sake jaddada matsayar ƙasar akan rikicin yankin Falasɗinu, inda ya bayyana cewa Gaza yanki ne na ƙasar Falasdinu kuma bai kamata a dinga cinikayyar siyasa da ita ba ko kuma wasu daga waje su dinga juya ta ba.

Jiokun ya yi wannan kalami ne a matsayin martani ga Shugaban Amurka Donald Trump, bayan ya yi ikirarin cewa ƙasar Amurka za ta mallake yankin na Gaza.

Ofishin jakadancin ƙasar Sin ne ya wallafa wannan jawabin na sa, yau Asabar a babban birnin tarayya Abuja.

Inda ya kuma bayyana cewa rikicin da ya ke wakana yanzu haka a yankin na Gaza, ya ɗaiɗaita yankin da kuma jefa su cikin wahala, inda ya bukaci hukumomin duniya musamman manyan kasashe, su haɗa guiwa don bayar da agaji da kuma tallafin sake gina yankin.

Ya kuma bayyana cewa ƙasar ta Sin, tana bayar da cikakken goyon bayanta ga ƴancin Falasɗinawa, da kuma sukar duk wani yunƙuri na kwashe mazauna yankin na Gaza.

Leave a Reply

%d bloggers like this: