Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya naɗa Umar Ibrahim a matsayin sabon sakataren gwamnatin jihar Kano, inda zai fara aiki daga ranar Litinin mai zuwa.

Mai magana da yawun gwamnan Sunusi Bature Dawakin Tofa ne ya tabbatar da naɗin, cikin wata sanarwa da ya fitar a daren jiya Asabar.
Sabon sakataren gwamnatin Umar Ibrahim ya kasance gogaggen ma’aikacin gwamnati, wanda ya shafe tsawon shekaru 30 a fannin.

Inda ya fara aikin gwamnati a shekarar 1987 zuwa 2023, bisa ƙwazo da nuna jajircewa da bayar da gudunmawa ga kafa tubalin shugabanci a jihar Kano.

Mai magana da yawun gwamnan ya bayyana cewa, Umar Ibrahim ya samu shaida da yarda daga gwamna Abba Kabir Yusuf, bisa tsawon shekarun da ya shafe ya na aikin al’umma.
Inda ya ce sabon sakataren gwamnatin ya kasance a manyan kwamitoci a baya, kuma ya taka muhimmiyar rawa wajen kawo sauyi a ɓangaren al’umma da kuma ilimi.