Hukumar hasashen yanayin sararin samaniya ta Najeriya (NiMet), ta yi hasashen samun yanayin hazo daga yau Lahadi zuwa ranar Talata a ɗaukacin faɗin Najeriya.

Hasashen yanayin hukumar da aka bayyana jiya Asabar a birnin tarayya Abuja, ya gano cewa za a samu madaidaicin yanayin hazo mai ɗauke da ƙura a yau Lahadi, a yankin arewa zuwa arewa ta tsakiya na ƙasar.
Inda hasashen ya bayyana yanayin zai fi shafi wasu ɓangarori na Jihohin Yobe, Kano, Katsina, Gombe, Bauchi, Kaduna, Jigawa da jihar Neja.

Sai kuma wani ɓangare a jihohin Kogi, Kwara da Binuwai, da za su fuskanci yanayin gajimare da kuma hazo.

Yayin da a yankin kudancin ƙasar kuwa, za a samu yanayin gajimare da hasken rana jefi-jefi a ɗaukacin jihohin yankin.
NiMet ta kuma bayyana cewa, za a samu hadari da tsawa a wasu yankunan Jihohin Legas, Ogun, Oyo, Cross River, Akwa Ibom, Ribas, Bayelsa, Ondo, Edo da kuma jihar Delta.