Asusun tallafawa yara na UNICEF ya yi kira ga gwamnatin jihar Kano, da ta haɓaka ƙoƙarinta a ɓangaren yaƙi da cutar shan-inna ta hanyar tsawaita bayar da rigakafi.

Babban wakilin UNICEF a Kano Rahama Farah ne ya yi wannan kiran jiya Lahadi a Kaduna, a wajen taron wayar da kai akan magance cutar shan-inna ga shugabannin kananan hukumomi 44 da dagatai da ke faɗin jihar.
Farah ya kuma jaddada cewa akwai bukatar samar da kudiri mai dorewa a siyasance, dan a tabbatar da cewa dukkan yaran jihar sun karbi cikakken rigakafin cutar na tsawon rayuwarsu.

Ya kuma ƙara da cewa jihar Kano ta zamto jihar mai muhimmanci dangane da kokarin kasa Najeriya na magance matsalar cutar, inda har yanzu akwai barazana a wasu yankunanta.

A Jawabinsa tunda fari Kwamishinan lafiya na jihar Abubakar Labaran Yusuf wanda ya kasance a wajen taron, ya sake tabbatar da irin kokarin da gwamnatin ta ke yi dan kyautata harkokin kiwon lafiya.