Akalla mutane 12 suka rasa rayukansu a yayin wani hadarin mota da ya afku akan hanyar Lapai zuwa Agaie a Jihar Neja.

Hadarin da ya faru a yau Asabar ya rutsa da maza Takwas Mata Hudu.

Wani shaidan gani da ido ya shaidawa Jaridar Daily Trust cewa mata uku daga cikin wadanda hadarin ya rutsa da su ‘yan gida guda ne.

A yayin hadarin direban motar da wasu fasinjoji mata biyu sun tsallake rijiya da baya, inda aka mika su ga Babban Asibitin garin Lapai.

Rahotannin sun bayyana cewa hadarin ya faru ne bayan wata arangama da motar ta yi da wata mota Kirar bas mai dauke da fasinjoji 15 tare da wata tirela a daidai Kauyen Nami a Jihar.

Kwamandan Hukumar Kiyaye afkuwar Hadurra FRSC ta Jihar Kumar Tsukwam ya tabbatar da faruwar lamarin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: