Jami’an sojin Najeriya hadin gwiwa da jami’an ‘yan sanda da na Sa-kai sun samu nasarar kubtar da wasu mutane 25, da shanu 22 da awaki Tara, bayan ‘yan bindiga sun sace a Jihar Neja.

Mai sharhi akan sha’anin tsaro a yankin tafkin Chadi Zagazola Makama ne ya tabbatar da hakan ta cikin wata wallafa da ya fitar a yau Asabar.

 

Jami’an sun samu nasarar ne ta cikin wani sumame da suka kai akan ‘yan ta’addan a Kauyukan Garun-Gabas da ke Kundu a Karamar hukumar Rafi ta Jihar.

Makama ya ce nasarar ta samu ne bayan samun bayanan sirri akan ‘yan ta’addan, inda hadin gwiwar jami’an suka kai sumame gurin a jiya Juma’a 21 ga watan Fabrairun nan, wanda hakan ya sanya suka samu nasarar.

Acewarsa bayan zuwan jami’an gurin sun yi musayar wuta da maharan wanda hakan ya tilasta musu tserewa, zuwa cikin ta, hakan kuma ya bai’wa jami’an tsaron damar kubtar da mutane da ke tsare a hannun ‘yan bindigar.

Makama ya ce mutanen da aka kubtar sun hada da maza da Mata, kuma ‘yan ta’addan sun kwaso su ne a kauyukan daban-daban na Jihar, inda kuma aka kai su sansanin sojin domin kula da lafiyarsu kafin mayar da su gidajensu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: