Shugaban Kasa Bola Tinubu ya yi kira ga al’ummar da su amfani da wananan wata na Ramadan wajen gudanar da addu’o’in neman zaman lafiya da ci gaba mai dorewa a Najeriya.

Shugaban ya bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa ta ya al’ummar musulmi barka da shigowa watan Azumi na Ramadan.
Acewar shugaban watan Ramadan wata ne na gudanar da ibada, hakuri da kuma tausayawa masu bukata da sadaukarwa.

Shugaban ya kuma kara jaddada aniyar gwamnatinsa na kara inganta fannin noma a Kasar don tabbatar da wadatuwar abinci ga al’ummar Kasar a lokacin watan azumin na Ramadan.

Shugaban ya ce gwamnatinsa na ci gaba da kara daukar matakan bunkasa bangaren noma don tabbatar da wadatuwar abinci ta hanyar bayar da tallafi da kuma kawo karshen yunwa a fadin Kasar, da kuma samar da dabarun noma na zamani.