Ruwan sama da guguwa masu ƙarfi sun yi sanadin rayukan Mutane biyar yayin da wasu da dama su ka jikkata.

An samu mamakon ruwan ne mai tafe da ƙaƙƙarfar iska da guguwa a Damaturu dake jihar Yobe a jiya Litinin 9 ga watan Mayun 2022.

Sakataren hukumar ba da agajin gaggawa na jihar Mohammed Goje ya tabbatar da afkuwar lamarin inda yaa ce fiye da gidaje 100 ne suka lalace sakamakon iftila’in.

Mohammed Goje ya ce sun samu labarin lamarin ne daga wasu mutane waɗanda suka taimaka wajen gaggawar kai waɗanda suka jikkata zuwa asibiti.

Mohammed Goje ya ƙara da cewa mutum biyar daga cikin 41 da lamarin ya rutsa da su sun mutu, kuma mutanen sun fito ne daga yankuna daban-daban a birnin Damaturu, inda aka wuce da su asibiti.

Yankunan da abin ya shafa sun haɗa da Waziri Ibrahim Extension da Abbari Extension da NayiNawa da Pompomari da rukunin gidajen ƴan majalisar dokokin jiha da Gujba Road da kuma Maisandari.

Leave a Reply

%d bloggers like this: