Gwamnatin tarayyar Nijeriya tasha alwashi taimaka wa ƙasar Sudan ta Kudu a yaƙi da ƴan Ta’adda da kuma haɗin kan ƙasar.

Shugaba Muhammad Buhari ne bayyana hakan ne a yau Juma’a yayin da ya karɓar baƙuncin wakilin Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir a fadar da ke Abuja.
Wakilin na musamman, Albino Matham Ayuel, ya yi wa Buhari bayani kan yadda wata ƙungiyar masu ta da ƙayar baya ta addabe su.

Albino ya bayya cewa ƴan Ta’addan kamar Boko Haram ɗinku ta aikata kashe-kashe kuma ta wulaƙanci da lalatawa.

Shugaba buhari yace za mu duba halin da kuke ciki don ganin yadda za mu taimaka.
Buharin ya bayya hakan cikin wata sanarwa da kakakinsa Fe mi Adesina ya fitar.
Sanarwar ta ƙara da cewa daga baya kuma ya nemi “haɗin gwiwa kan tsaro, musamman ba wa dakaru horo tun da kuna da ƙwarewa kan wannan lamari”.
[contact-form][contact-field label=”Name” type=”name” required=”true” /][contact-field label=”Email” type=”email” required=”true” /][contact-field label=”Website” type=”url” /][contact-field label=”Message” type=”textarea” /][/contact-form]