Wata majiya mai ƙarfi ta bayyana cewa mai girma gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya haƙura da neman kujerar Sanata a zaɓe mai zuwa.

Gwamnan ya ɗauki wannan matsaya ne a sakamakon sasantawa da aka yi tsakanin ɓangaren sa a APC da kuma tsagin Sanata Barau Ibrahim Jibrin.
Kamar yadda mu ka samu rahoto, an yi zaman sulhu ne a daren ranar Lahadi da ta gabata a birnin tarayya Abuja.

A ƙarshen zaman sulhun da aka yi, Abdullahi Umar Ganduje ya haƙura da zuwa majalisa, ya kyale Jibrin ya sake neman kujerarsa.

Ahmed Prince Gandujiyya, ɗaya daga cikin magoya bayan ɗan majalisar, ya tabbatar da wannan labari da yake magana a shafin Facebook yau da safe.
Shi ma Abubakar Aminu Ibrahim wanda Hadimi ne wajen Gwamnan Kano, ya nuna labarin ya tabbata, ya daura hoton da ke nuna Ganduje ya hakura.