Hukumar daƙile cin hanci darshawa a Najeriya ta ce ta sake gano wasu maƙudan kuɗaɗe da dakataccen akantan Najeriya ya yi sama da faɗi da su.

Binciken da hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ke gudanarwa kan dakataccen Akanta-Janar na Tarayya, Ahmed Idris ta gano kudin da su ka kai naira biliyan 170.

Ahmed Idris, wanda ke fafutukar neman beli a daren jiya Lahadi, ya magantu kan wasu manyan jami’an gwamnati da ake zargin suna da hannu a hada-hadar kudin.

Hukumar RFCC ta yiwa wani sakataren din-din-din tambayoyi da ke da alaka da wasu badakala da sunansa ya fito a ciki.

Jami’an EFCC sun gano wasu abubuwa masu ban mamaki game da hada-hadar kudi a ofishin babban Akanta na tarayyar.

Rahotanni sun nuna cewa da farko ana tuhumar babban akantan da badakalar naira biliyan 80 ne, bayan da bincike yayi nisa aka sake gano akwai wata badakalar ta naira biliyan 90.

Akwai alamu da ke nuna cewa babban akantan ya yiwa EFCC alkawarin mayar da wasu kudade zuwa asusun gwamnati.

Leave a Reply

%d bloggers like this: