Sabuwar kungiyar ta’addanci ta jama’atu Ansarul muslimina fil biladi ta sanar da cewa ba ta da hannu a harin jirgin kasan da aka yi a Jihar Kaduna a watan Maris din da ya gabata.

Kungiyar Ansaru ta bayyana hakan ne a ranar Alhamis.
Kungiyar ta rarrabawa matafiya wasu takardu dauke da bayanan barranta kansu daga kai harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa Daga cikin bayanin da kungiyar ta Ansaru ta rubuta da harshen Hausa ta bayyana cewa kungiyar su ba ta kaiwa matafiya jirgin kasa hari ba, sai dai su na kaiwa gurbatacciyar gwamnati domin tsaida adalci aban kasan.

Ansaru ta kara da cewa burinsu shine su kare musulmai da aka zalunta da ma wadanda su ke cikin matsin rayuwa.
Kungiyar Ansaru ta karyata jita-jitar da ake yadawa cewa wani mai suna Abu Barra shine shugaban kungiyar, sun ce ba haka ba ne,inda su ka ce nan bada jimawa ba za su sanar da shugabansu.
Wani shugaban matasa a birnin Gwari da ya nemi a sakaye sunan sa ya bayyana cewa mayakan kungiyar Ansaru sun bayyana da rana tsaka suna rabawa mutane matafiya takardu masu dauke da bayyanan.