
‘Yan sandan babban birnin tarayya Abuja sun tarwatsa wasu masu zanga-zanga a birnin tarayya Abuja a jiya Juma’a.
Masu gudanar da zanga-zangar sun kasance ‘yan uwan fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ne da ‘yan bindiga su ka yi garkuwa da su.

‘Yan uwan fasinjojin su na gudanar da zanga-zangar ne don ganin gwamnatin tarayya ta kubtar musu da ‘yan uwan nasu da ‘yan bindigan su ka sace.

Masu zanga-zangar su na dauke da allunan rubutu inda su ke kira ga shugaban kasa da ya taimaka ya kawo musu dauki.
Daya daga cikin ‘yan uwan fasinjojin mai suna Abdulmumin Muhammad ya bayyana wa manema labarai cewa ba su ji dadin korar da jami’an tsaron su ka yi musu.
Abdulmumin ya ce har yanzu ba su gamsu da kokarin da gwamnati ta ke yi don ganin ta kubtar da mutanen ba sannan yayi kira ga gwamnatin da ta gaggauta kubtar da yan uwansu.
Jami’an ‘yan sandan sun bayyana cewa dalilin da ya sanya su ka fatattakin masu zanga-zangar saboda ba su sanar da su cewar za su gudanar da zanga-zangar ba.