Hukumar yaki da hana sha da fataucin miygun kwayoyi a Najeriya NDLEA reshen Jihar Kogi ta kama mutane 149 da ta ke zargi da shan kwayoyin da ma safarar su.

Hukumar ta ce ta kama mutanen ne a cikin watanni shida.

Sanann hukumar ta kwace miyagun kwayoyi wanda suka kai kilo 1,966 tun daga watan Junairu zuwa watan Yuni da muke ciki.

Kwamanda hukumar reshen Jihar Kogi Abdulkadir Abdullahi fakai shine ya bayyana haka a yau Talata ga manema labarai a wani bangare na gudanar da ranar yaki da shan miyagun kwayoyi ta duniya.

Taron na bana an masa taken yaki da shan miyagun kwayoyi ya kan cutar da lafiya.

Kwamandan ya ce wadanda ake zargin sun hada mata da maza kuma an kwace kayyakin mate a wajensu.

Daga cikin ƙwayoyin da aka kamma akwai Taramadol Cocaine Exol 5. Diazepam Cannabis Sativa da dai sauran kayan da ke sanya maye.

Sannnan mutane 29 daga cikin su har yanzu ana ci gaba da gudanar da shari ar su a babbar kotu dake Lokoja.

Ya kara da cewa shan miyagun kwayoyin a Jihar ta Kogi abun ya yawaita har ma ya bukacu muhukunta su kara tunkarar wanann matsalar don kawo karshenta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: