Daga Yahaya Bala Fagge

Ƙungiyar musulmai a Najeriya ta MURIC ta roki hukumar jarrabawar fita daga Makarantar sakandire wato NECO da ta sauya ranar Tara ga wata domin rubuta jarrabar sakamakon bikin babbar Sallah.

Shugaban kungiyar Ishaq Akintola shine aike da rokon a yau inda ya ce ranar Asabar da Hukumar NECO ta sanya ranar ce da duk musulmin Duniya ke gudanar da bikin Sallah don haka su ka bukaci sauya ranar tare da
sanya wata daban.

Ishak ya ce ranar Asabar bai dace da ranar da za aje domin rubuta jarrabawa ba, yana mai rokon hukumar NECO da ta sauya tare da sanya wata ranar.
Hukumar NECO ta sanya Ranar Asabar Tara ga watan da mu ke ciki a matsayin ranar da za a rubuta jarrabawar a Najeriya.
Sai dai shugaban ya ci gaba da cewa ya san NECO ba ta na sane ta yi hakan ba domin har kusan mako ɗaya ta baiwa dalibai na hutun jarrabawa domin gudanar da bikin sallah daga ranar 11 zuwa 15 na watan Yuli da muke ciki.