Rundunar ƴan sandan jihar Osun ta bayyana cewa za ta tsaya tsayin daka domin ganin an gudanar da tsaftataccen zaben gwamnan Jihar ba tare da sayan kuri’u ba.

Rundunar hadin gwiwa da sauran jami’an tsaro a Jihar sun tabbatar da cewa matukar su ka kama dukkan mai yasan kuri’u a zaben za su dauki tsatstsauran mataki akan sa.
Rundunar ta “yan sandan ta ce a yayin zaben da ya ke gabata sun yi wasu tsare-tsare wanda zai taimaka musu domin kama masu yasan kuri’un.

Rundunar ta kuma kara da cewa daga cikin jami’an tsaron da za su gudanar da ayyuka a gurin zaben ciki harda jami’an tsaron farare kaya domin sanya idanu a gurin zaben.
