Jami’an Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC sun yi dirar mikiya a kasuwar chanji ta Zone 4 a birnin tarayya Abuja domin kama wadanda su ka boye dala.

Jami’an su kai sumamen ne sakamakon wasu “yan kasuwar da su ke boye dalar Amuruka wanda hakan ke sanyawa farashin kayayyaki ya ke tashi a Najeriya.
Jami’an sun ce yin hakan da “yan kasuwar su ka yi ya haddasa faduwar naira a kwanakinna.

Ba tun yanzu ba jami’an sun dade su na sanya idanu akan yan kasuwar ta chanji dala wanda su ke boyewa daga bisani su fitar da ita kasashen ketare.

Bayan zuwa kasuwar yan chanjin da jami’an na EFCC su ka yi hukumar ta sake aike da jami’an ta Filayen Jiragen sama na Jihar Kano da Legas da kuma garin Part Horcort domin damke masu shirin fita da dalar kasahen ketare.
Hukumar ta EFCC ta tura jami’an ne sakamakon faduwar farashin Naira da aka yi a Jiya Alhamis wanda ba a taba samu ba, yayin da ita kuma dala daya ta kai Naira 705 a kasuwar chanji.