Tsohon gwamnan Jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi gargadi ga wasu daga “yan majalisar dokokin Najeriya wadanda su ke yunkurin tsige shugaban Kasa Muhammad Buhari daga kan Karagar Mulkin Najeriya da su bi a hankali.

Sanata Kwankwaso ya bayyana hakan ne bayan wata ziyara da ya kaiwa gwamnan Jihar Kwara a Ilorin babban birnin Jihar.

Kwankwaso ya kara da cewa bai kamata sanatocin su daukin matakin hakan da gaggawa ba.

Ya ce duk da “Yan majalisar su na da hujjojin su akan matsalar rashin tsaro ce da ta addabi kasar.

Sanata Rabiu Kwankwaso ya yi kira ga gwamnatin Tarayya da ta kara kaimi akan matsalar rashin tsaro domin ganin an maganceta.

Sanata Kwankwaso ya bayyana cewa ya kamata gwamnatin ta tattauna da wadanda su ke da alaka wajen magance matsalar rashin domin samo hanyoyin da za a bi domin a magance matsalar baki ɗaya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: