Gwamnatin jihar Kano ta tabbatar da a shirin da take domin ganin ta yi adalci ga malamin makarantar nan, Abdulmalik Tanko da aka yankewa hukuncin kisa.

Jaridar The Guardian ta nuna Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje a shirye yake domin ganin an tabbatar da adalci ga masu laifin kisan.
Babban lauyan gwamnatin Kano, Musa Lawan ya bayyana cewa wasu suna tunanin ba za a hukunta wadanda aka samu da laifin kashe Hanifa ba.

A watannin baya ake zargin wasu mutane da laifin hallaka karamar yarinya mai shekara 5. A watan Yuli ne aka tabbatar masu da laifinsu.

A ranar Alhamis, Musa Lawan ya shaidawa mutanen Kano cewa wadanda aka yankewa hukunci za su dandana kudarsu.
Kwamishinan shari’a yake cewa hukumar gidan gyaran hali za ta bayar da shaidar tabbatar da hukunci, wanda zai fito bayan wa’adin daukaka kara.
Akwai kwanaki 90 da doka ta ba wadanda ake kara da nufin su daukaka shari’a idan ba su gamsu da hukuncin da Alkalin kotun tarayya ya zantar ba.
Idan ba a daukaka kara ba, gwamna zai sa hannu, idan kuwa an koma kotu, za a saurari shari’a.