Yayin da kungiyar malaman jami’o’i suka shafe akalla watanni bakwai suna yajin aiki shugaba kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci su hakura su janye .

Rahoton da aka samo ya bayyana cewa, Buhari ya bayyana hakan ne a taron bikin karrama Alhaji Muhammadu Indimi, shugaban kamfanin Oriental Energy Resources Ltd a birnin Maiduguri na jihar Borno.

An gudanar da wannan babban taro ne a cikin jami’ar Maiduguri, daya daga cikin manyan makarantun Najeriya da ke garkame sakamakon yajin da ASUU keyi.

Shugaban ya samu wakilcin shugaban ma’aikatansa Alhaji Ibrahim Gambari, wanda ya zanta kan batutuwa da yawa da suka shafi ilimi a Najeriya.

Da yake tuna batun ASUU tare da yin tsokaci a kai, Gambari ya isar da sakon Buhari da cewa

Yana da kyau su ce wani abu game da wannan yajin aikin na ASUU saboda suna karrama Alhaji Indimi wanda aka shirya wa gagarumin biki a yau domin ci gaban ilimi mai inganci da ya kawo ba a kasar nan kadai ba.

A kan haka, yana so ya isar da kiran shugaban kasa Muhammadu Buhari game da ASUU da ta janye yajin aikin da take yi, ta koma aiki.

Abangare guda, Buhari ya ce tuni tattaunawa tsakanin ASUU da gwamnati akeyi, amma duk da haka kungiyar ta ci gaba da bude makarantu.

Ya kuma koka da cewa, bai dace ASUU su ci gaba da ajiye dalibai a gida ba kasancewar abubuwa sun kasa kankama.

A cewarsa, irin wannan tsawaita wa’adin yaji na dakushe ilimi tare da kawo cikas ga ci gaban mutane.

Leave a Reply

%d bloggers like this: