Hukumar kiyaye afkuwar haɗɗura a Najeriya FRSC na shirin fara yi wa masu baburan haya risjita.

Kwamandan hukumar a yankin Okitipupa a jihar Ondoo ce ta bayyana haka yayin ganawa da manema labarai yau Talata.

Ta ce wannan matakin an ɗauka ne da nuin taimakawa ɓangaren tsaro yadda za a daƙile wasu yyukan da ake aikatawa da babura.

Sannan matakin rijistar da za a yi wa babura za a yi en a dukkanin jihohin Najeriya domin daƙile miyagun ayyukan da ake fama da su.

Za a fara rijistar ne ga masu baburan haya kuma hukumar za ta fara kama waɗanda ba u yi rijistar ba kamar yadda za a fara a nan gaba.

Ta ce rashin yi wa baburan da ake haya da su ne ya sa ake iya aikata wasu miyagun laifuka da hakan ke ci gaba da kawo barazana ga tsaro a Najeriya.

Shugabar ta shawarci masu baburan haya da su bi dokokin da ake yi na rijistar don kaucewa fushin hukuma.

Leave a Reply

%d bloggers like this: