Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana cewa a zaben shekarar 2023 mai zuwa za ta jajirce wajen ganin an yi sahihin zabe.

Hukumar ta tabbatar wa mutane cewa ba za ta bari a yi magudi a gurin zabe ba.

National Peace Committee NPC da Cibiyar The Kukah Centre su ne su ka shirya wani taron a birnin tarayya Abuja dangane da gabatowar zaben.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa Farfesa Muhammad Kuna mataimaki na musamman ga shugaban hukumar zabe ta kasa shi ne ya bayyana hakan a yayin taron.

A yayin taro Janar Abdulsalam shi ne ya kasance shugaban Kwamitin NPC mai wanzar da zaman lafiya yayin da Bishof Methew ya ke jagorantar Cibiyar Kukah.

Taron wanda ya kasance na karawa juna sani wanda aka gudanar a birnin Tarayya Abuja a ranar Talata tare da tattaunawa akan yadda fasahar zamani za ta taimaka a yayin zaben.

Farfesa Kuna ya ce amfani da fasahar zamani ta BVAS za ta taimaka matuka a lokacin zaben.

Ya ce a yayin zabe ma’aikatan zabe su na tura adadin kuri’a da sakamakon zabe daga kowacce mazaba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: