Tsohon gwamnan jihar Kano kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar NNPP Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce babu jam’iyyar da zai janyewa takarar shugaban kasa a zaɓen 2023.

Kwankwaso ya bayyana haka ne a yayin ganawa da yan jarida a Maiduguri babban birnin jihar Borno ranar Lahadi.

Ya ce akwai wasu mutane da su ke tsammanin zai janyewa wani ɗan takara ko jam’iyya daga shugabanci, sai dai ya ce hakan ba ya daga cikin tsarinsa.

“Batun jam’iyyar NNPP za ta janyewa PDP ko APC zallar shirme ne” inji Kwankwaso.

Ya ƙara da cewa akwai wasu da su ke tsammanin siyasarsa iya jihar Kano ce ya ce ya na alfahari da hakan domin Kano babban gari ne.

Ya kara da cewa a ƙasa da watanni shida jam’iyyar NNPP ta karaɗe ko ina kuma ba wanda ya san me za ta zama a nan gaba.

Kwankwaso ya ci gaba da cewa a yanzu ƴan Najeriya sun fara fahimtar cewa ƙasar ta ɗauki hanyar rushewa kuma hakan a bayyane yake a fili.

Leave a Reply

%d bloggers like this: