Wasu da ake zargi ‘yan daba ne sun kone gidan da mambobin mmabiya mmazahabar Shi’a ke amfani da shi wurin taro, karatu da ma’ajiyar kayayyaki a nguwar Dorayi babba dake karamar hukumar Gwale ta jihar Kano.
Daily Trust ta rahoto cewa, shugaban cibiyar, Dr Sulaiman Gambo ya bayyana hakan ga manema labarai a Kano.
Yace ‘yan daban sun tsallaka ta katanga kuma suka kone ginin da ma’ajiyar kayayyakin da suka kai darajar kudi naira miliyan uku.
Gambo yace a ranar 2 ga watan Augusta da ya gabata an kai wa mambobinsu farmaki yayin da suke wani taro inda aka raunata biyar tare da kone motarsu.
Sannan ya yi kira ga hukumomin da lamarin ya shafa da su zakulo miyagun dake wannan mugun aikin wadanda suka sha alwashin hana ‘yan Shi’a damarsu ta bauta kuma a bi musu hakkin su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: