Akalla mutane biyu ne su ka rasa rayuwakan su tare da ceto mutane bakwai a lokacin da wani jirgin kwale-kwale ya nitse da su a cikin karamar hukumar Miga ta Jihar Jigawa.

Jam’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Jihar Lawan Shisu Adamu shi ne ya bayyana farwar lamarin.
Kakakin ya ce Lamarin ya farune a lokacin da wasu manoma su tara su ke kokarin komawa gidajen su daga gonakinsu a kauyen Galauchime zuwa garin Sansani da ke karamar hukumar ta Miga a Jihar.

Lawan Shisu ya kara da cewa manoman sun hau jirgin Kwale-kwale ne wanda wani mai suna Ado ya ke tukawa bayan hawan su jirgin ya kife da su sakamakon ruwan sama da iska da aka yi.

Ya ce bayan afkuwar lamarin an samu nasarar ceto mutane bakwai yayin da mutane biyu kuma su ka rasa rayukansu.
Kakakin ya bayyana cewa mutane biyun da su ka mutu daya dan 14 ne daya dan shekara 12 ne inda su ka mikawa iyayensu domin yi musu sutura.