Wani matashi dan shekara 37 mai suna Munkaila Ahmadu, ya hallaka mahaifansa a kauyen Zarada-Sabuwa da ke karamar hukumar Gagarawa ta jihar Jigawa.

Kakakin yan sandan jihar, Lawan Shiisu Adam, ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ya fitar jiya Alhamis.

Lawal Adam ya ce Munkaila ya yi amfani da tabarya wajen doke mahaifinsa, Ahmad Muhammad mai shekaru 70 wanda shine hakimin kauyen da kuma mahaifiyar Hauwa Ahmadu mai shekaru 60.

Matashin ya farmaki wasu mazauna yankin biyu, Kailu Badugu mai shekaru 65 da kuma Hakalima Amadu mai shekaru 50.

Kakakin yan sandan ya ce da samun rahoton al’amarin su ka aike da tawagar jami’an yan sanda wajen da aka aikata laifin sannan suka kwashe wadanda abun ya ritsa da su zuwa babban asibitin Gumel.

Likita ya tabbatar da mutuwar Ahmadu Muhammad da Hauwa Ahmadu sakamakon raunin da suka ji a kansu yayin da aka kwantar da Kailu Badugu da Hakalima Ahmadu wadanda suka ji rauni daban-daban.

Kakakin yan sandan ya ce an kama wanda ake zargin sannan an kwato makamin.

Binciken farko ya nuna cewa Ahmad Muhammad da Hauwa Ahmadu sune suka haifi wanda ake zargi.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Jigawa Aliyu Sale Tafida, ya bayar da umarnin mika lamarin zuwa sashen binciken manyan laifuka na jihar da ke Dutse, domin gudanar da bincike mai zurfi tare da gurfanar da mai laifin a gaban kotu bayan kammala bincike.

Leave a Reply

%d bloggers like this: