Gwamnan Jihar Borno Babagana Umara Zulum ya bai wa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri UMTH na Jihar tallafin naira Miliyan 100 tare da ginawa ma’aikata gidaje 24 a cikin Asibitin.

Gwanan wanda ya kaddamar da mika kudadan tare da kaddamar da ginin gidajen ma’aikatan Lafiya a ranar Juma’a.
Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatinsa na yin hakan ne domin bai wa ma’aikatan gudunmawa bisa jajircewar da Asibitin ya ke a gurin jinyar marasa lafiya a da ke Jihar.
Gwamnan ya ce Asibintin wanda ya kasance mallakin gwamnatin tarayya gidajen da za a gina a cikin sa za su kasance masu dakuna uku-uku sannan za a kammala su a tsayin watanni shida masu zuwa.

Gwamnan Zulum ya kara da cewa hakan ne ya sanya ya cire kudaden domin domin bai wa masu aikin ginin gidajen domin ginawa ma’aikatan don magance matsalar gidajen likitocin a cikin Asibitin tare da kawo su kusa da marasa lafiyan.

A nasa bangaren shugaban Asibitin koyarwa na Jami’ar Farfesa Ahmad Ahidjo ya jinjinawa gwamnan dangane da gudummawar da ya ke bai wa Asibitin domin samar da ingantattun kayan aiki a cikin Asibitin.
Farfesa Ahmad ya ce taimakon da gwamnatin Jihar ta ke bai wa Asibitin al’ummar Jihar ba za su taba manta wa da shi na.