Wani matashi mai shekaru 15 a duniya ya kashe abokin sa ta hanyar caka masa wuka a lokacin da wani rikici ya barke a tsakanin su a karamar hukumar Rimin Gado da ke Jihar Kano.

Matashin yaron ya hallaka abokin nashi ne a jiya juma’a bayan sabanin ya shiga tsakaninsu a yayin da su ke kallon suloka.

Yaron ya ce ya dauki matakin hakan ne a lokacin da dan uwan fadan nasa ya soki ra’ayinsa inda ya nemi da su je wani kebantaccen guri domin su fidda raini.

A lokacin da su ka isa gurin yaron ya fito da wukar da ya ke sana’ar yankan rake ya caka masa a kirji a lokacin da yaron ya rufe shi da duka.

Bayan faruwal lamarin aka nufi da yaron da aka cakawa wukar zuwa Asibitin Murtala inda zuwan su ke da wuya likitoci su ka tabbatar da mutuwar yaron.

Leave a Reply

%d bloggers like this: