Hukumar zabe mai zaman kanta INEC tace yanzu haka akwai korafe korafe 600 a gaban kotuna daban daban dake kakubalantar zabukan fidda gwanin jam’iyyu.
Shugaban hukumar Farfesa Mahmud Yakubu ne ya bayyna hakan a yayin taron bita ga alkalai kam al’amuran da suka shafi babban zabe na 2023.

Yakubu ya ce hukumarsa ta yi nazarin hukunce-hukuncen kotuna daban daban da akayi tun daga zabukan fidda gwani na gwamnoni, hadi da na cike gurbi da aka gudanar har zuwa yanzu.
farfesa yakubu yace sungano wuraren daya kamata su kawo gyara don rage yawan shigar da kara, kuma sakamakon haka, an sami kaguwar kararraki dake kalubalantar zabukan da hukumar ta gudanar.

sai dai yace kararrakin zabukan da jam’iyu suka gudanar na karuwa sosai, domin ko makwanni biyu da suka gabata sai da wata jam’iya ta shigar da korafi 70, tana nema INEC ta amince mata ta yi nadi ko sauya ‘yan takarkaru, duk kuwa da cikar wa’adin yin hakan a jadawalin zaben 2023.

ya ci gaba da cewa matsalar na kawo cikas ga shirye shiryen gudanar da babban zabe, da su kansu kotunan dole za su ci gaba da wasu shara’ar har bayan zabe.