Shugaban kasa Muhammadu Buhari na Najeriya ya bayyana kaduwa da samun labarin yadda wasu ‘yan ta’adda suka yiwa basaraken gargajiya, Eze Ignitus Asor na yankin Obudi-Agwa a jihar Imo kisan gilla a makon nan.

Bayan yin Allah-wadai, Buhari ya umarci jami’an tsaro da su gano wadanda suka aikata wannan mummunan aiki tare da tabbatar da doka a kansu.

Idan baku manta ba, rahoto ya bayyana yadda wasu ‘yan ta’adda suka hallaka basaraken a jihar Imo.

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu ya fitar, Buhari ya ce ya yi Allah wadai da wannan kisa da yan bindiga suka yi.

Yayin da yake mika ta’aziyya ga iyalai da ‘yan yankin Obudi-Agwa, Buhari ya kuma yiwa wadanda suka raunuka a harin fatan samun lafiya cikin gaggawa.

Hakazalika, ya yaba da kokarin gwamnan jihar Imo wajen haka fannin tsaro tare da karfafawa mazauna jihar gwiwar ci gaba da ba gwamnati hadin kai wajen zakulowa tare da gurfanar da masu aikata laifuka.

Yankin Kudu maso Gabas na daya daga yankunan da ake fama da hare-haren ‘yan ta’adda a ‘yan shekarun nan, ana zargin ‘yan IPOB da tada zaune tsaye a yankin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: