A yau Alhamis kotu taci gaba da shar’ar kisan matashiyar nan mai suna Ummukulsum Sani Buhari, wadda ake zargin masoyinta dan kasar china, Geng Quangraong da kashe ta a jihar Kano.

Kotun ta cigaba da sauraron shaidu a shari’ar bayan ta saurari bayanin mahaifiyar da aka kashe da kuma kanwar marigayiyar a jiya laraba.
An gabatar da karin shaidu daga makwafta da sauran mutane da suka halarci wurin da abin ya faru, domin kafa hujja kan tuhumar da akeyi wa dan Chinan.

Bayan da lauyoyin bangarorin biyu suka gabatar da tambayoyi ga shaidun da aka gabatar, Daga karshe alkalin kotun ya dage sauraron shariar zuwa gobe Jumaa don cigaba da karbar shaidu.
