Gwamnatin tarayya ta dawo da darasin tarihi a makarantun Firamare da na Sikandire bayan da ta soke shi tun a shekarar 2009.

Babban sakataren hukumar ilmi matakin farko, Malam Hamid ya ce an dauki malamai dari-dari daga dukkan jihohi 36 na kasar har da babban birnin tarayya Abuja.
Da yake jawabi yayin kaddamar da dawo da darasin da kuma horas da malaman, Ministan ilmi Malam Adamu Adamu ya ce dakatar da darasin da aka yi a baya ya haifar da karuwar lalacewar tarbiya da raya al’adu.

Adamu Adamu ya bayyana hakan ne ta bakin karamin Ministan ilmi, Goodluck Opiah wanda ya wakilci Ministan a yayin taron.

A nasa jawabin mai alfarma sarkin musulmi Dr. Sa’ad Abubakar lll, ya gargadi sarakunan gargajiya da sauran ‘yan Najeriya da su taimaka tare da goyon bayan gwamnati kan dawo da darasin tarihi a makarantun Firamari da na Sikandiri a fadin kasar.