Babbar kotun jihar kano ta yankewa Abduljabbar hukuncin kisa ta hanyar rataya bulsa kama shi da kalaman batanci ga Annabi Mahammadu.

Alkalin kotun mai Sharia Ibrahim sarki yola shi ne ya bayyana hukunci yau da da misalin karfe 1;00 na rana a kotun .

Sarki yola ya ce bisa hujjojin da suka bayyana a gabansa na wanda ake Kara kuma ya kasa kare kansa a bisa tuhumomin da ake masa ya yanke hukuncin kisan.

Sannan Abduljabbar abin da ake zargin sa da ya fada a cikin karatuttukansa kuma ya kasa kare kansa bisa kin nuna inda bayanin yake a littafi.

Ibrahim Sarki yola ya ci gada cewa ya na mai umartar gwamnatin kano da ta rufe masallatansa guda biyu Ashabul khafi da Rasulun Ameen. dake filin mushe.

Kuma ya ce ya kwace litttafansa Abduljabbar guda 189 da ya ke kafa hujja da su a wajen karatu.

Kuma alkalin kotun hana yada karatunsa a katafen sadarwa na Radio da na TV.

Daga karshe dai Abduljabbar ya na da damar daukaka kara a babbar kotun daukaka kara ta kano zuwa kwanaki 30 a cewar alkalin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: