Majalisar Dattawa  a Najeriya ta bukaci Babban Bankin Nijeriya (CBN), da ya sake duba manufofinsa kan tsarin takaita cirar kudade day a gabatar.

Babban bankin a karkashin sabon tsarin cire kudi, ya takaita yawan kudaden da mutane da kamfanoni za su rika cirewa duk mako daga N100,000 zuwa N500,000.

Sai dai majalisar dattijai bayan ta yi la’akari da rahoton kwamitinta kan harkokin banki, wanda ya hada baki da shugabannin bankin CBN kan wannan manufa, ta bukaci bankin da ya daidaita ka’idojin fitar da kudi duba da koke-koken jama’a da ya biyo baya.

Majalisar ta kuma umarci kwamitinta da ya fara sa ido a kan babban bankin CBN kan kudirinsa na daidaita kai rahoto ga majalisar dattawa lokaci zuwa lokaci.

Har ila yau, majalisar ta kuduri aniyar tallafa wa babban bankin a ci gaba da aiwatar da ayyukan samar da canji da kuma ayyukan masana’antu da hada-hadar kudi kamar yadda ya dace da dokar CBN

Leave a Reply

%d bloggers like this: