Rundunar ‘yan sandan Jihar Ogun sun samu nasarar kama wasu ‘yan damfara ta kafar Intanet bisa zargin su da yin garkuwa da abokin aikin su.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Abimbola Oyeyemi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Alhamis.
Abimbola ya ce sun kama mutanen ne a ranar Litinin a kauyen Orile Imo da ke cikin karamar hukumar Obafemi Owode ta Jihar.

Kakakin ya kara da cewa sun kama su ne bayan samun bayanin batan wani mai suna Haruna Usman wanda ya kasance abokin aikin mutanen.mutanen

Oyeyemi ya bayyana daga cikin mutanen sun kama mutane hudu yayin da biyu su ka tsere.
Kazalika ya ce mutanen sun yi garkuwa da Harune sakamakon kin ba su kudin da ya damfara naira miliyan 26 inda ya ba su naira miliyan 2.2.
Kakakin ya ce da zarar sun kammala bincike za su gurfanar da su a gabab kotu domin yi musu hukunci.