Rundunar ‘yan sandan Jihar Kwara ta kama wani matashi da yayi garkuwa da mahaifinsa har ta kai ga ya anshi kudin fansa.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Okasanmi Ajaye shine ya tabbatar da faruwal lamarin.


Ajaye ya bayyana cewa an kama matashin ne a yankin Unguwar Kumbi da ke Ilori babban birnin Jihar.
Kakakin ya kara da cewa jami’ai a sashin yaki da masu garkuwa na rundunar ne su ka samu nasarar kama wanda ake zargi a lokacin da su ka bi sahun wasu da ake zargi masu garkuwa da mutane ne.
Ajaye ya ce wanda ake zargin ya karbi har naira miliyan biyu da rabi a matsayin kudin fansar mahaifinnasa.
Jami’in ya bayyana cewa kawo yanzu jami’an rundunar su na ci gaba da gudanar da bincike domin kamo sauran mutanen da su ka tsere.
Bayan kama wanda ake zargi ya amsa dukkan laifin da ake tuhumar sa dashi,inda ya ce ya hada baki da wasu mutane biyu har ta kai gaya sace mahaifinnasa a Jihar Oyo.
Kakakin ya ce za su aike dashi ga rundunar ‘yan sandan Jihar Oyo domin fadada bincike akansa.